Arsenal ta sanar da cewa Cedric Soares da Takehiro Tomiyasu da Ainsley Maitland-Niles duk sun kamu da cutar korona.
‘Yan wasan Ukun ba a saka su a cikin ‘yan wasan da Arsenal ta buga da Norwich City a gasar Premier ranar Lahadi ba, saboda su na zaman kadaici na killacewa.
Cedric da Tomiyasu da Maitland-Niles sun bi takwarorinsu Albert Sambi Lokonga da Pablo Mari da Calum Chambers wajen yin gwajin cutar Korona a cikin makonni biyun da suka gabata.
Mari da Chambers sun dawo daga cikin wadanda a ka maye gurbinsu da tafiya zuwa Carrow Road, amma Chambers bai halarci wasan ranar wasan ba.