fidelitybank

Korona: Mutane 3 sun mutu ta sanadiyar daskarewar jinni a New Zealand

Date:

A kalla mutum uku ne aka tabbatar da mutuwarsu ta sanadiyyar daskarewar jini bayan sun

Hukumar kula da ingancin allurar rigakafin COVID-19 ta kasar ce ta sanar da hakan, a ranar Litinin, inda ta ce, mutanen sun mutu ne sakamakon matsalar daskarewar jinni bayan an yi musu allurar rigakafin.

Kan wannan batun ne hukumar ta zauna, domin tattauna korafe-korafen da a ke samu, domin a gano ko su na da alaka da rigakafin ko kuma a’a.

Mutanen da suka mutu dai sun hada da wani yaro mai shekara 13, da wani matashi mai shekara 26 da kuma wani tsoho mai kimanin shekara 60.

Sai dai hukumar ta ce, ya zuwa yanzu ba ta kai ga gano alaka tsakanin allurar da daskarewar jinin a jikin tsohon mai shekara 60 ba, sannan ta na bukatar karin bayani, domin tantance rawar da rigakafin ta taka a mutuwar yaron mai shekara 13.

Sanarwar ta kuma kara da cear, bisa ga bayanan da su ka tattara, sun gano cewa daskarewar jinin ta faru ne a jikin wannan matashin mai shekara 26 sakamakon rigakafin.

Rahotanni dai sun ce matashin ya fara nuna alamun cutar ne ’yan kwanaki kadan da yi masa rigakafin, sannan ya mutu cikin mako biyu da karbar zagaye na farko na allurar.

Hukumar dai ta amince cewa matsalar ta daskarewar jini na daga cikin illolin da a ka fi fuskanta daga rigakafin na Pfizer, amma ta ce ita kanta COVID-19 din na iya haifar da matsalar daskarewar jinin. A cewar kamfanin dillancin labarai na NAN.

thisdaynews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da É—anyen man kaÉ—anya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaÉ—a labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp