A na sa ran ‘yan wasan Manchester United za su koma daukar atisaye a filin wasan su na Carrington a ranar Laraba.
Manchhester United ta rufe bangaren rukunin farko na filin atisayen ta a ranar Litinin, bayan da a ka dage wasan da za su yi da Brentford a gasar Premier ranar Talata.
An sake yi wa tawagar ‘yan wasan da su ka dawo gwaji za su iya komawa daukar horo.
Wasan United na gaba shine da Brighton a Old Trafford a ranar Lahadi.