Hukumar tsaron farin Kaya ta (DSS) ta sanar da cewa ’yan majalisar dokoki na tarayya na fuskantar barazanar garkuwa domin neman kudin fansa ko kuma kisa.
DSS ta bayyana hakan ne a daidai lokacin da ’yan majalisar da sauran ’yan Najeriya ke shirye-shiryen tafiya hutu, domin bukukuwan karashen shekara.
Mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya ne ya sanar da hakan, ya na mai cewa, “Wadannan mutane suna cikin hadarin kisa da sacewa da garkuwa da su ko yi musu fashi tare da yi musu surkullen siyasa”. inji Peter Afunanya.
Karon farko ke nan da hukumar ta ambaci ’yan Majalisar Tarayya kai-tsaye a jerin mutanen da ke cikin hadarin garkuwa da su ko yi mu kisan gilla a Najeriya.
A baya hukumar kan yi wa ’yan majalisar kudin goro ne a cikin manyan mutane idan ta tashi fitar da gargadin jerin mutanen da ke cikin hadari ko barazanar tsaro.
A baya-bayan nan dai an ji wasu daga cikin ’yan Majalisar suna kokawa cewa lamarin matsalar tsaro a yankunan da su ke wakilta ta kai makura ta yadda su da kansu ba sa iya zuwa garuruwansu.
DSS ta bukaci ’yan majalisar da ’yan siyasa da ma’aikatan gwamanti da sauran jama’a cewa, su kasance masu lura da yanayin tsaro, domin kar Su fada cikin hadarin hari da miyagun makirce-makirce. Inji Aminya.