Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, ya yaba da halayen ‘yan wasansa, bayan da suka doke Ajax da ci 2-1 a gasar zakarun Turai ranar Talata.
Reds ta yi rashin nasara a wasansu na farko na rukuni da ci 4-2 a Napoli.
Bayan wannan sakamakon a Naples, Klopp ya bukaci martani daga ‘yan wasansa.
Mohammed Kudus ne ya zura kwallon da Mohamed Salah ya ba shi, kafin Joel Matip ya ƙara kwallon ta biyu.