Mabiya addinin shi’a sun ziyarci majami’ar mabiya addinin Kirista, domin halartar bukukuwan Kirsimieti.
Da ya ke jawabi a wata hira da manema labarai jim kadan bayan kammala hidimar, shugaban kungiyar, Farfesa Isa Mshelgaru ya ce, makasudin halartar taron shi ne bunkasa soyayya, hakuri da fahimtar juna a tsakanin ‘yan Najeriya.
Ya ce, “Mun yanke shawarar halartar wannan hidimar coci, domin yau ce ranar Kirsimeti, ranar da ake bikin zagayowar ranar haihuwar Yesu a dukan duniya, kuma muna jin cewa muna son mu gaya musu abubuwan da su ka ji a ranar haihuwar sa.
“Zuwan Yesu duniya albarka ce ga kowa da kowa, domin haka muna fata mu zo mu yi bikin wannan rana mai daraja tare da su.”
Ya ce a matsayin su na musulmi suna daukar kiristoci a matsayin ’yan uwansu a cikin bil’adama, ya na mai jaddada cewa, suna hidimar cocin ne, domin hada kai da su wajen gudanar da bukukuwa da kuma raba musu farin cikin wannan rana.
“Wannan ya na da mahimmanci a yanzu da kasar ke fuskantar kalubalen tsaro da yawa wadanda ke bukatar dukkan hannaye su kasance a kan wasu, domin shawo kan su,” inji shi.
A sakonsa ga sauran ‘yan Najeriya, Mshelgaru ya shawarci ‘yan Nijeriya su hadu ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabilanci ko siyasa ba, domin ceto al’ummar kasar baki daya.