fidelitybank

Kayan asibiti na daga da ƙarewa a Gaza – Ma’aikatar Lafiya

Date:

Ma’aikatar Lafiya ta Zirin Gaza ta yi gargaɗin cewa awa 48 kacal suka rage kafin dukkan kayayyakin aikin lafiyar da take da su su ƙare a yankin sakamakon datse hanyoyin shiga da fita da Isra’ila ta yi.

Sanarwar da ta fitar na cewa ba za ta iya ci gaba da ayyuka a asibitoci ba saboda tashar lantarki tilo da take bai wa Gaza wuta ta rufe saboda rashin man fetur da take fama da shi.

Yanzu haka asibitocin na aiki ne da ƙananan injinan lantarki, waɗanda ke fama da ƙarancin man su ma.

Ya zuwa yanzu, ma’aikatar lafiyar ta ce, an jikkata Falasɗinawa 215, yayin da jiragen Isra’ilar ke ci gaba da ruwan wuta a kan unguwannin Gaza.

Isra’ila ta ce tana harar mayaƙan ƙungiyar Palestinian Islamic Jihad ne, amma hare-haren sun kashe fararen hula 32 zuwa yanzu. In ji BBC.

sspdf news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...

Trump ya yaudari Amurkawa da Iran – Aragachi

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana cewa...

Sai an hukunta Mutanen da suka kashe ƴan ɗaurin aure – Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi Alla-wadai da...

An fara binciken fashewar wani abu da ya kashe mutane 5 da jikkata da dama a Kano

Wani abin fashewa da ake tunanin bom ne ya...

An samu fashewar wani abu a kamfanin ƴan Chana a Kano

An samu fashewar wani abu a Kamfanin Ƙarfe na...

Ma’aikacin kamfani ya kashe abokin aikinsa a Kano

Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ya...

Kotu ta ɗaure Matashin da yake tare titi a Kano da sunan barƙwanci

Kotun majistire da ke unguwar Nomansland a Kano, karkashin...

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama ƴan Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...
X whatsapp