fidelitybank

Kasafin Kudi: El-Rufa’I zai kashe Naira biliyan 6 a manyan asibitoci

Date:

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai’s ya ware Naira biliyan 6, domin inganta kayan aiki ga manyan asibitoci a fadin jihar Kaduna a shekarar 2022.

Hakan ya nuna cewa cikin kasafin kudin 2022 na Naira biliyan 278.6 da El’-Rufa’I ya sanyawa hannu.

A cikin kasafin kudin na 2022 na Naira biliyan 278.6, za a kashe Naira biliyan 15.7 ga ma’aikatar lafiya, inda za a kashe Naira biliyan 7.4 wajen gina da kuma samar da kayan aikin asibitin kwararru mai gadaje 300.

Gwamnatin Kaduna ta kuma ware Naira miliyan 51.6, domin ginawa tare da gyara bangaren karbar agajin gaggawa na manyan asibitocin Kafanchan da Saminaka da Birnin Gwari da Hajiya Gambo Sawaba.

Kasafin kudin ya kuma hada da gina sabuwar kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma a Pambegua, wadda za ta samu Naira miliyan 281.7.

Takardar ta nuna an ware Naira miliyan 17.4 domin samar da firinjin adana jini guda 20.

Takardar ta kuma nuna cewa an ware Naira miliyan 370, domin gina cibiyar kula da masu fama da rauni a Doka, yayin da a ka ware Naira miliyan 28.9, domin kula da kayan aikin jinya a cibiyoyin lafiya na matakan lafiya a farko 31.

Sannan ya nuna cewa an ware Naira miliyan 861.7 a matsayin takwaran aikinsa na shirin yaki da cutar zazzabin cizon sauro, domin karfafa tsarin rigakafi da abbatar da inganci da kula da ingancin tantance cutar zazzabin cizon sauro da magani.

Hakazalika, za a kashe Naira miliyan 62.6 kan cutar tarin fuka mai jure wa magunguna, Naira miliyan 188 kan shirin samar da abinci mai gina jiki na gaggawa na Kaduna da kuma Naira miliyan 50 a karkashin tallafin samar da abinci mai gina jiki da bankin duniya ke tallafawa a Najeriya.

 

 

nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp