Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta rage wa direbobin baburara masu taya uku wanda aka fi sani da Adaidaita Sahu kuɗin sabunta takardar shaidar izinin tuƙi daga Naira 8,000 zuwa Naira 5,000.
Mai magana da yawun hukumar, Nabilusi Abubakar Ƙofar Na’isa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Tun a ranar 10 ga watan Janairu, 2022 ne direbobin baburaran Adaidaita Sahu suka tsunduma yajin aikin gargaɗi, sakamakon rashin amincewarsu da biyan Naira 8,000 a matsayin kuɗin sabunta takardar shaidar izinin tuƙin da kuma sauran batutuwa.
Hukumar ta ce, ta kuma rage kuɗin sabuwar izinin tuƙi daga Naira 18,000 zuwa Naira 1,500.
Wannan matakin ya biyo baya ne, tun kammala wani zaman sulhu da ta yi da lauyoyin direbobin baburaran Barista Abba Hikima Fagge.
Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Jihar Kano, Aminu Sani Gadanya ne ya jagoranci lauyoyi a wajen zaman sulhun.
A cewar KAROTA, matuƙa baburan za su biya waɗannan kuɗaɗe ne daga nan zuwa ƙarshen watan Fabrairu, 2022.