Kotu a kasar Italiya ta kama tsohon ɗan wasan Brazil, Robinho, da laifin yi wa wata mata fyade.
Kotun Ƙolin da ke birnin Rum ta aminta da hukuncin kotun ɗaukaka kara da ta yanke wa Robinho da abokansa biyar hukuncin daurin shekara tara.
A shekarar 2013 aka zargi Robinho da abokansa da cin zarafin wata yar kasar Albania ta hanyar lalata, a lokacin da ya ke wasa a kungiyar kwallon kafa ta AC Milan.
Amma da wahala ya sha ɗauri, lura da cewa ɗan ƙwallon ya na ƙasarsa kuma Brazil ba ta da yarjejeniyar mika dan kasarta, domin fuskantar hukunci a wata kasa.
Robinho wanda tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da AC Milan da kuma Manchester City da kuma Newcastle a nahiyar Turai.