Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasa NUPENG, ta zargi gwamnatin tarayya da laifin karancin man fetur a kasar nan.
NUPENG ta ce karancin man fetur ya samo asali ne sakamakon gazawar fifikon gwamnati.
Da yake jawabi yayin taron wakilai karo na 5 na kungiyar direbobin tankar mai (PTD) reshen NUPENG a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, shugaban kungiyar, Kwamared William Akporeha, ya ce, maimakon dora laifin karancin man fetur a kan direbobin tankar man fetur ba kowaba ne illa gwamnati, wanda ya c,e ta ki gina sabbin matatun mai a cikin shekaru 30 zuwa 40 da suka wuce.
Akporeha ya ce: “Me ya sa ake karancin man fetur? Ina samfurin yake? Karancin ba direbobin tanka ne suka haddasa shi ba, sai dai rashin fifikon gwamnati. Idan samfurin yana samuwa, membobi zasu motsa shi.
“Ta hanyar shigo da kayan, kuna fitar da jari, kuna fitar da ayyukan yi ta yin hakan.
“Ba na jin kimiyyar roka ne yin hakan. Matatun man da muke da su a yau sojoji ne suka gina su shekaru 30 zuwa 40 da suka wuce.”