fidelitybank

Kano: EFCC ta kama matasa Uku da katin ATM 1,144

Date:

Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC), ta kama wasu mutane Uku da ake zargi a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA), a lokacin da suke kokarin safarar katinan kudi na ATM 1,144 zuwa kasar waje.

Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren, ya ce wadanda ake zargin akwai, Abdullahi Usman da Musa Abubakar da kuma Abdulwahid Auwalu, an kuma kama su ne tsakanin ranar 24 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga Disamba, 2021 ta hannun jami’an ofishin hukumar na jihar Kano.

An gano cewa Abubakar da ke kan hanyarsa ta zuwa kasar hadadiyar daular larabawa Dubai, ya boye katin ATM guda 714, yayin da Usman da ke kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya, ya na da katin ATM guda 298 a hannunsa.

A daya bangaren kuma, an kama Auwalu da katin ATM 132 a lokacin da yake kokarin shiga jirgin kasar Habasha zuwa birnin Santanbul na kasar Turkiyya.

Hukumar EFCC ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar ta kammala binciken ta.

assu update

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp