Jam’iyyar APC, reshen jihar Ebonyi, ta ce gwamnan jihar, Dave Umahi ya na nan a jam’iyyar zama daram, kuma babu wata jam’iya da zai koma.
Jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar APC a jihar Ebonyi, Simbard Ogbuatu, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a birnin Abakaliki.
Ya ce”Jam’iyyar APC a Ebonyi ta samu labarin da ya karade kafafen yada labarai da rubutun farko na sama ya na cewa “Orji Kalu da Umahi na yunkurin komawa PDP” wanda Dr Isaac Nkole, jigo a PDP a Abia ya wallafa. Umahi ya na nan a jam’iyyar APC, saboda haka jama’a da su yi watsi da wannan labari a matsayin ‘kwatancin wanda ya fito”. Inji Simbard.