fidelitybank

Kannywood: Ban cinye kudin kowa ba – Sadik Sani Sadik

Date:

Kotun shari’ar musulunci da ke Hotoro Masallacin Juma’a a Jihar Kano, ta bayar da umarnin a kamo mata shahararren jarumin fina-finan Hausa na Kannywood a Najeriya, Sadiq Sani Sadiq, bisa zargin saɓa alƙawari da ya yi.

Tun da farko wani mai shirya fina-finai, Aliyu Muhammad Hannas ne ya shigar da ƙarar a gaban kotun, inda ya ke ƙorafin cewar ya baiwa jarumin kuɗi domin ya yi masa aikin film, amma yaƙi zuwa don yin aikin.

Mai ƙarar ya kuma yi ƙorafin cewa ƙin yi aikin da Sadiq ya yi ya ja masa asara mai yawa.

Alkalin Kotun, Maishari’a Sagiru Adamu, yace Sadiq ya bijirewa umarnin kotu duk da sammacin da aka bashi, tare da liƙe masa sammacin a bangon gidansa, amma yaki halartar zaman kotun.
Wanda hakan ne ya sanya alkalin ya baiwa jami’an ƴan sandan kotun umarnin kamo jarumin a duk inda ya ke zuwa gaban kotun.

Haka kuma ko tun ta ce da zarar an kamo jarumin masana’antar Kanywood ɗin za a cigaba da zaman sauraren shari’ar.

Da ya ke zantawa da manema labarai, Sadiq ya ce ba mai shirya fim ɗin ba ne ya bashi kuɗin kai tsaye ba.

Sadiq ya ƙara da cewa Naira dubu ɗari a ka bashi a matsayin wani ɓangare na kuɗin kwantaragin fim ɗin.

In da ya ce, shi ba cinye masa kuɗi ya yi ba, hasali ma bai san ko wanene mai fim ɗin ba, tunda ba kai tsaye su ka kulla yarjejeniyar ba.

nigeria news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp