fidelitybank

Kamfanin NNPC ya samu zunzurutun kudi Naira Biliyan 203.73 a watan Yuli

Date:

Kamfanin Man Fetur na (NNPC), ya ce reshensa na kasa ya samu zunzurutun kudi har Naira Biliyan 203.73 kan siyar da fararen kaya a watan Yulin 2021.

Wannan ya na kunshe ne a cikin alkalumman watan Yuli na shekarar 2021 na rahoton kudi da ayyuka na kamfanin NNPC na watan (MFOR), bugu na 72 na rahoton da aka fitar ranar Laraba.

Rahoton ya nuna karuwar kashi hudu cikin 100 na samar da iskar gas.

Rahoton ya kuma bayyana cewa jimlar kudaden shiga da a ka samu daga siyar da kayayyakin na tsawon watan Yulin 2020 zuwa Yuli 2021 ya kai sama da tiriliyan 2.563 inda Premium Motor Spirit (PMS) ta ba da gudummawar kusan kashi 99.67 na jimillar tallace-tallace.

Hakazalika, jimillar lita biliyan 1.544 na kayayyakin man fetur ne hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa PPMC ta sayar da kuma rabar da su, a watan Yuli da PMS ya kai kashi 99 cikin 100 na adadin man fetur.

Rahoton ya kuma kara da cewa, Jimillar siyar da kayayyakin man fetur na tsawon watan Yuli 2020 zuwa Yuli 2021 ya tsaya a kan lita biliyan 19.535 kuma PMS ya kai kashi 99.73 na jimillar adadin.

naija hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp