fidelitybank

Kaddara ce ta shigo da ni siyasa – Zulum

Date:

Gwamnan jihar Born, Babagana Umara Zulum, ya ce, shi ba dan siyasa ba ne, ƙaddara ce ta shigar da shi siyasa.

Zulum ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da jaridar Daily Trust ta shirya a Abuja wanda aka yi wa take “siyasa, tattalin arziki da tsaro”.

An shirya taron ne gabanin zaben 2023 domin tattaunawa kan makomar Najeriya, kuma ya samu halartar manyan baki kamar su tsohon shugaban kasar na mulkin soji Janar Abdulsalmi Abubakar da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, da Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III da kuma shi kansa Zulum da dai sauransu.

“Duk da cewa ni ne gwamnan Borno a yanzu, tsautsayi ne ya sa na zama, kuma ba wai cin dunduniyar ‘yan siyasa nake ba domin zan bar kujerar da nake a nan gaba. A yanzu da nake gabanku, kuma muke tunkarar 2023, kalubalen da yake gabanmu ba na wane ne za a zaɓa ba a matsayin kaza ba, a’a kalubalen shi ne wane ne ya cancanci matsayi kaza”.

“Zai yi wu da yawanku sun ɗara ni shekaru, amma ba ni da burin riƙe wani mukami sama da wanda na ke rike da shi a yau, sai dai idan kaddara ce Allah Ya rubuta min. Ba za mu cimma gaci ba, har sai mun ajiye bambanci a gefe, mun nemi wadanda suka cancanta, shi ne za mu iya samun shugabanni da suka dace”. In ji Zulum

the sun newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp