fidelitybank

Kaddara ce ta shigo da ni siyasa – Zulum

Date:

Gwamnan jihar Born, Babagana Umara Zulum, ya ce, shi ba dan siyasa ba ne, ƙaddara ce ta shigar da shi siyasa.

Zulum ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da jaridar Daily Trust ta shirya a Abuja wanda aka yi wa take “siyasa, tattalin arziki da tsaro”.

An shirya taron ne gabanin zaben 2023 domin tattaunawa kan makomar Najeriya, kuma ya samu halartar manyan baki kamar su tsohon shugaban kasar na mulkin soji Janar Abdulsalmi Abubakar da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, da Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III da kuma shi kansa Zulum da dai sauransu.

“Duk da cewa ni ne gwamnan Borno a yanzu, tsautsayi ne ya sa na zama, kuma ba wai cin dunduniyar ‘yan siyasa nake ba domin zan bar kujerar da nake a nan gaba. A yanzu da nake gabanku, kuma muke tunkarar 2023, kalubalen da yake gabanmu ba na wane ne za a zaÉ“a ba a matsayin kaza ba, a’a kalubalen shi ne wane ne ya cancanci matsayi kaza”.

“Zai yi wu da yawanku sun É—ara ni shekaru, amma ba ni da burin riĆ™e wani mukami sama da wanda na ke rike da shi a yau, sai dai idan kaddara ce Allah Ya rubuta min. Ba za mu cimma gaci ba, har sai mun ajiye bambanci a gefe, mun nemi wadanda suka cancanta, shi ne za mu iya samun shugabanni da suka dace”. In ji Zulum

vgn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu É—auki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta É—aukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...

Ba mu kai wa Isra’ila hari ba – Iran

Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ƙasar...

Duk da faduwar farashin mai NNPCL ya kara farashi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin...

Duk wasu Ć™awayen Amurka za su É—anÉ—anar kuÉ—arsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...

Iran ta mayar da martani kan sojojin Amurka dake Qatar

Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ƙasar ta...

Faransa ba ta goyon bayan Amurka na kifer da gwamnatin Iran – Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce, ƙasarsu ba ta...

Kotu a Kano ta É—aure masu satar Yara

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller...

Ba wata hujja da Amurka za ta kai wa Iran hari – Rasha

An gudanar da tattaunawa tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin...

Tinubu ya miĆ™a saĆ™on ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...
X whatsapp