Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bar Najeriya zuwa birnin Nairobi ranar Juma’a, domin sa ido a zaben Kenya.
Tsohon shugaban na jagorantar tawagar masu sa ido a babban zaben kasar da za a gudanar a ranar 9 ga watan Agusta.
Jonathan shi ne shugaban tawagar sa ido kan zabe na cibiyar zabe don dorewar dimokradiyya a Afirka (EISA).
Mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze ya ce, tawagar EISA ta kunshi masu sa ido na gajeren lokaci 21 da aka zabo daga kungiyoyin farar hula.
Tawagar ta ƙunshi hukumomin gudanar da zaɓe da wakilan cibiyoyin ilimi daga sassa daban-daban na Afirka.
Eze ya lura cewa, za a tura masu sa ido a dukkan yankuna musamman a kananan hukumomi goma na Kenya.


