fidelitybank

Jita-Jita: Da gaske ne Aisha Buhari ta na da juna biyu?

Date:

Sabbin Hotunan Uwargidan Shugaban Najeriya, A’isha Buhari na kara rura wutar jita-jitar da ke ta bazuwa na daukar ciki a fadin kasar, inda ‘yan Najeriya ke tunanin ko da gaske cewa za ta haihu.

People’s Gazette ta rawaito cewa daya daga cikin hotunan da jaridar ta fitar ta ce, Aisha Buhari tare da mijinta, shugaban kasa Muhamadu Buhari, sun kewaye jami’an tsaro, daya daga cikinsu dauke da jakar hannu.

A cikin wata kaftan lace mai launin rawaya da bakar abun rufa da aka lullube da abin da ya zama kamar na jariri, wanda Aisha Buhari mai shekaru 50 ta dora hannunta na dama a kan cikin ta.

A cewar jaridar mutane na ta tofa albarkacin bakin su a kan wannan batu, domin kuwa wani hoto ya nuna ma’auratan farko suna zaune a cikin jirgin sama. Wani zuzzurfan tunani da a ka yi wa Aisha Buhari ya nuna cikakkiyar fuska irin ta mace mai juna biyu, daban da na baya da a ka saba.

Hoto na uku ya nuna ma’auratan a kan matakalar jirgin, da alamun jinjiri yayin da uwargidan shugaban kasar ta sauka a hankali.

Kalamun da ke ta mayar da martani daga shafukan sada zumunta na cewa, “Aisha Buhari ta na da ciki ko abin da ke cikinta,” inji wani mai amfani da shafin Twitter @Promise.

Shi ma wani mai amfani da shafin Twitter, @Solowizzy ya yi tsokaci a kan hotunan, inda ya ce, “Yan Najeriya me ku ke tunani kan wadannan hotuna? Babu shakka Aisha Buhari na da ciki.”

A wani sako mai ban dariya da ya wallafa a shafinsa na Twitter, @Alamin97296003 ya taya Buhari mai shekaru 79 murna kan “kwazonsa”.

“Aisha Buhari ta na da ciki. Baba Buhari mai aiki tukuru,” inji mai amfani da Twitter.

Idan ta na da ciki, Mrs Buhari, wacce ta riga ta zama kaka, za ta kasance matar shugaban kasa ta farko da a ka san ta na da juna biyu a lokacin da mijinta ke kan mulki, kuma mai yiwuwa ita ce ta fara haihuwa a fadar shugaban kasa.

Tun a shekarar 2016 ne a ka fara fitowa fili cewa Aisha Buhari ba ta ji dadin yadda mijinta ke tafiyar da al’amuran kasar nan ba. A wata hira da ta yi da sashen Hausa na BBC, ta yi ikirarin cewa an sace gwamnatin Buhari.

A cewar rahoton na Fabrairu, ta ziyarci Daura tare da Buhari a ranar 9 ga Maris, 2019, a lokacin zaben shugaban kasa.

A wani martani da Aisha Buhari ta ce,”Shugaban kasa bai san 45 daga cikin 50 na mutanen da ya nada ba, kuma ni ma ban san su ba, duk da kasancewar matar sa ta shekara 27,” inji ta.

 

opra news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp