fidelitybank

Jita-Jita: Babu batun komawa jam’iyyar PRP daga APC – Gwamnatin Kano

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta musanta jita-jitar da ke yawo cewar gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje da tawagarsa na shirin sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PRP.

Jita-jitar ta biyo bayan ganawar da ɓangaren APC na gwamnan ke yi a ƙoƙarin ɗaukaka ƙara kan hukuncin da wata kotu ta yi a Abuja game da zaben shugabanin jam’iyyar a mazabu da kananan hukumomin Kano.

Hukuncin kotun na ranar Juma’a ya baiwa ɓangaren Shekarau da ke rikici da ɓangaren gwamna Ganduje nasara.

Sai dai mai shari’a Hamza Muazu wanda ya zartar da hukuncin ya kuma buƙaci ɓangaren gwamna Ganduje da ke neman a yi watsi da shugabancin ɓangaren Shekarau ya biya tarar miliyan ɗaya.

An danganta shirin gwamnan na sauya sheka daga jam’iyyar ta APC, sakamakon hukuncin wanda ya ƙara zafafa rikicin APC a Kano tsakanin ɓangaren gwamnan da na tsohon gwamna Sanata Shekarau.

Sai dai cikin wata zantawa da BBC Hausa da kwamishinan raya karkara na jihar, Musa Iliyasu Kwankwaso, wanda ya na ɗaya daga cikin jiga-jigan ɓangaren na Ganduje, ya ce, batun ba shi da wani tushe ballantana makama.

Ya kara da cewa ,”Jam’iyyar APC ta mu ce, kuma za a ci gaba da kokarin yin sulhu, domin rikicin siyasa ba sabon abu ba ne kuma za a zo a daidaita idan har wadanda ke rikicin da su na nan cikin jam’iyyar ba su fita ba”

vgn news today 2021

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp