Gwamnatin kasar Amurka ta ce kudurin ta na aniyar tallafawa shirye-shiryen da ke inganta da ilimin kafafen yada labarai.
Da ya ke jawabi a wajen bikin bude taron bitar a jihar Legas a ranar Litinin, jami’in hulda da jama’a na ofishin jakadancin Amurka, Stephen Ibelli ya bayyana cewa, ingantacciyar dimokuradiyya na bukatar dukkanin jama’a da a ka sa ni da kuma kafafen yada labarai masu kishin kasa wadanda ke ba da bayanai na gaskiya da gaskiya.
Shirin dai tare da goyon bayan Babban Ofishin Jakadancin Amurka a Legas da Cibiyar yada labarai ta Afirka ta Yamma (WABMA) da Enugu Literacy Society (ELS), sun kaddamar da shirn na “Project Fact Check Nigeria,” wani aikin jarida da kuma magance rashin fahimta na zakulo bayanan gaskiya.
Aikin ya na neman ƙarfafa dabarun tunani, faɗaɗa ilimin zamani na dijital da kafofin yada labarai da haɓaka ƙarfin ƴan jaridun rediyo, domin magance munanan labarai da na ɓarna a jahohi 17 na kudancin Najeriya.
Sama da masu yada shirye-shiryen rediyo 170, ciki harda furodusoshi, da masu ba da rahoto za su sami ƙwarewar bincikar gaskiya da na mafi kyawun ayyuka, domin kaucewa yada labaran kanzon Kurege da kuma rashin fahimta.
“Ta hanyar inganta ilimin kafofin yada labarai, mu na ƙarfafa ka’idodin gaskiya, shugabanci nagari da kuma bin doka da ke aiki a matsayin ginshiƙan tsarin dimokuradiyyar mu,” inji Ibelli.