fidelitybank

Jirgin Kasa yayi awon gaba da Tirela da babur din Adaidaita Sahu a Kano

Date:

A na fargabar wasu fasinjojin sun mutu, yayin da wani jirgin kasa da ke tafiya ya murkushe motar tirela ta Siminti ta Dangote da wani Babur din Adaidai ta Sahu mai kafa uku a jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a kan titin Obasanjo a cikin birnin Kano da misalin karfe 11:30 na safiyar Lahadi.

Shedun gani da ido da ke gudanar da sana’o’i a kusa da titin jirgin, sun ce, sun ga tirelar ta nufo layin dogo ne a lokacin da jirgin ke gudu.

Shaidu sun ce, sun yi yunkurin taimakawa tirelar, amma direban bai lura ba.

Jirgin kasan a lokacin da ya tsaya

“Lokacin da direban tirelar ya yi Æ™oÆ™arin ketare layin dogo, jirgin ya buge motar da babur É—in a lokaci guda,” in ji É—aya daga cikin shaidun.

Shaidu sun ce, tuni aka garzaya da fasinjojin da ke cikin babur din zuwa asibiti a sume, yayin da direban tirelar ya tsira da ransa.

Har ya zuwa lokacin da muke kawo wannan rahoton, tirelar har yanzu ta na kife a wajen wanda mutane suka zagaye  wajen, domin ganin bata gari basu kwashe buhunan siminti na cikin motar ba, yayin da jami’an tsaro suka baiwa motar kulawa, domin kar ‘yan ganima su kwashe kayan.

pulse news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp