Jiragen sama biyu na Yaƙin Duniya na II sun yi arangama a sararin samaniyar Texas ta Amurka, inda hatsarin ya yi sanadiyyar kashe mutum biyu.
Wani bidiyo ya nuna yadda jiragen suka yi karo da juna, jirgi ɗaya ya karairaye. An ga kuma yadda wuta ta tashi nan take yayin da yake faɗowa ƙasa.
Jiragen na shawagin tunawa da yaƙin ne a kusa da Dallas.
Babu tabbacin ko mutum nawa a cikin jirgin.
Ƙungiyar direbobin jirgi ta Amurka mai suna Allied Pilots Association ta ce mambobinta Terry Barker da Len Root na cikin mutanen da suka mutu a hatsarin.
Wasu kafofin yaɗa labarai na cewa waɗanda suka mutu sun kai shida.