Makonni biyu bayan karon da jirage biyu suka yi a Tokyo, babban birnin kasar Japan, an sake samun karon wasu jiragen biyu a ranar Talata.
A cewar kafar watsa labarai ta gwamnatin kasar ‘NHK’, lamarin ya faru ne a filin jiragen sama na New Chitose a Hokkaido da misalin karfe 5:30 agogon kasar.
Sai dai a wannan karon babu wanda hatsarin ya shafa.
A cewar NCHK, hatsarin ya faru ne yayin da jirgin Koriya Ta Kudu da na Hong Kong, Cathay Pacific suka yi karo a filin jiragen.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani jami’in kamfanin jirgin saman Koriyan na cewa, yayin da jirginsu ke tashi ya yi karo da na Cathay Pacific, kuma akwai fasinjoji 289 a cikin jirgin saman Koriya Ta Kudun.
Kafar watsa labarai ta NHK ta ambato kamfanin Cathay Pacific na cewa babu kowa a cikin jirginsa a lokacin da hatsarin ya auku.
An soke tashin jirage da dama a filin jiragen saman na New Chitose bayan an samu hatsarin.


