Fitacciyar ‘yar fim din nan ‘yar Iran, Taraneh Alidoosti, ta sanya wani hotonta, kanta a bude ba dan-kwali ko hijabi domin nuna goyon bayanta ga zanga-zangar da ake ta yi ta kin jinin gwamnatin Iran.
Matar ta kuma rike wani kwali da aka rubuta Mace Rayuwa, ‘Yanci a harshen kurdawa, wanda wannan kusan shi ne taken zanga-zangar da mutuwar wata matashiya Ba’kurdiya Mahsa Amini a hannun ‘yan Hisbah ta janyo.
Rahotanni na cewa tana daya daga cikin manyan fitattun mutane a cikin Iran da suka tari aradu da ka, suka fito fili karara suka goyi bayan masu zanga-zangar.
Tauraruwar ta fim tana da mabiya kusan miliyan takwas a shafinta na Instagram.