Tawagar ‘yansanda tare da hadin gwiwar sojojin Najeriya da ‘yan banga a jihar Kebbi, sun dakile wani harin ‘yan bindiga, inda suka kashe daya tare da kwato bindiga kirar AK47 a karamar hukumar Augie dake jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, Nafi’u Abubakar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi ranar Lahadi.
Abubakar ya ce rundunar ta samu labarin cewa a ranar Asabar da misalin karfe 3 na safe ‘yan bindiga da dama sun kai hari kauyen Tiggi da ke karamar hukumar Augie a jihar Kebbi.
Ya ce, “Bayan samun rahoton, rundunar ‘yan sandan da aka tura yankin tare da hadin guiwar sojoji da ’yan banga, nan da nan aka tattaro ‘yan banga inda suka yi artabu da ‘yan bindigar.
“Sakamakon haka, an kashe daya daga cikin ‘yan bindigar, kuma da yawa sun tsere da raunukan bindiga. Sai dai kuma an kwato bindiga kirar AK 47 guda daya.”


