Gwamnatin jihar Zamfara, ta ɗauki matakin shirya jami’an tsaro da za su riƙa sintiri a kan manyan titunan jihar.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce za a girke jami’an tsaron domin sintiri a kan hanyar Gusau zuwa Funtua da Magami zuwa Dangulbi zuwa Dan Kurmi da wasu tinunan da ake samun barazanar tsaro a jihar.
A taron majalisar tsaron jihar na baya-bayan nan da gwamnan jihar Dauda Lawan Dare ya koka wa shugabannin jami’an tsaro da ke jihar kan ayyukan ‘yan fashi a wasu manyan titunan jihar, ɗaya daga cikin dabarun da gwamnan ya ɗauka domin magance matsalar tsaro da jihar ke fuskanta.
Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an tsaron da za su yi sintiri a kan titunan sun haɗar da sojojin ƙasa da na sama.
Haka kuma sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta ce ta kammala shirye-shirye domin fara ɗauka tare da horas da ‘yan sa kai a jihar.


