Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya ta tabbatar da kisan riƙaƙƙen ɗan bindigar da ya addabi wasu yankunan jihar.
Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Ahmad Manga ya bayyana kisan Danbokolo a matsayin gagarumin nasara a yaƙi da matsalar tsaro.
”Danbokolo mutum ne da ya fi Bello Turji fitina, ya fi Turji aikata miyagun laifuka, illa kawai shi Turji sunansa da ya karaɗe kafofin yaɗa labarai”, in ji Ahmad Manga.
”Mutanensa da aka kashe sun haufa 100, saboda haka wannan gagarumar nasara ce a gare mu”, in ji jami’in gwamnatin Zamfarar.
Kacalla Danbokolo ya rasa ransa a wata arangama a ƙauyen Kurya, tsakanin jami’an sa kai na gwamnatin jihar Zamfara da mayaƙan ɗanbindigar.
Ana kallon mutuwar Danbokolo – wanda ake ganin a matsayin ubangidan Bello Turji – a matsayin cigaba a ɓangaren yaƙi da ƴanbindiga.
Donbokolo ya shafe shekaru masu yawa yana kai hare-hare yankunan jihar Zamfara tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.
Riƙaƙƙen ɗanbindigar ya gamu da ajalinsa ne tare da wasu ɗimbin mayaƙansa a lokacin da jami’an tsaron sa kai – da gwamnatin jihar Zamfara ta samar.
Mazauna yankin na kallonsa a matsayin mutum marar imani da tausayi da ya addabi yankunansu, ta hanyar kai hare-hare da kisan mutane.
“Shi mutum ne da bai yarda da sulhu ko ta wane hali ba, hatta ɗan’uwansa Bello Turji ya taɓa nuna alamun amincewa da sulhu, amma shi wannan bai taɓa nuna hakan ba”, kamar yadad wani mazaunin yankin ya bayyana.
Wannan ne karo na biyu da jami’an tsaro ke kashe riƙaƙƙun ƴanbindiga da ake ganin a matsayin iyayen gida da Bello Turji.
A watan Satumban 2024 ne jami’an sojojin ƙasar suka kashe Halilu Sububu, wanda ya shi ubangida ne ga Bello Turji a wani kwantan ɓauna da suka yi masa tare da mayaƙansa.