‘Yan ta’addar Daesh a lardin Yammacin Afirka, ISWAP, sun kashe dan sanda guda tare da dauke mota daya a wani hari da suka kai ofishin ‘yan sanda na Gubio a jihar Borno.
Wani kwararre a fagen yaki da masu tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wani sako da ya wallafa a shafin X.
A cewar Zagazola, ‘yan bindigar sun zo ne a kan wasu motoci kirar Hilux guda biyu da kuma babura da dama kafin su yi ta harbe-harbe, inda suka far wa ofishin ‘yan sanda.
Ya rubuta cewa majiyoyi sun tabbatar da cewa wani Sufeto na ‘yan sanda ya biya mafi girman farashi yayin da yake hulda da ‘yan ta’addan.
An kuma bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun yi awon gaba da wata mota kirar ‘yan sanda guda daya.


