Mayakan kungiayr, ISWAP, sun tare matafiya tare da yin awon gaba da su da bakin bindiga a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a ranar Asabar.
Kawo yanzu dai ba a tabbatar da adadin matafiyan da kungiyar ta yi garkuwa da su ba, a harin na misalin karfe 8.30 na safiya a yankin Benisheik.
Majiyar Aminiya ta ce, “Gaskiya ne an kai wa matafiya hari a safiyar nan a babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, inda wadannan mutanen su ka yi awon gaba da fasinjojin da ba a san adadinsu ba a tsaksain Benishiek da Mainok; Kawo yanzu dai ba mu da bayanai sosai.”
Sai dai shugaban Gamayyar Kungiyoyin Fararen Hula a Yankin Arewa maso Gabas, Ambasada Ahmed Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin.