Wani hari da Isra’ila ta kira ‘Operation Rising Lion’, da ta ce ta kaddamar da nufin wargaza shirin nukiliyar Iran, ya kashe manyan jami’an soja da ƙwararru a fannin nukiliyar ƙasar, kamar yadda rahotannin kafafen yaɗa labaran Iran suka ruwaito.
Ga jerin jami’an da aka tabbatar da mutuwarsu a harin na Isra’ila.
- Hossein Salami – Babban kwamandan rundunar juyin juya halin ƙasar (IRGC)
- Gholamali Rashid – Kwamandan hedikwatar Khatam-al Anbiya
- Fereydoon Abbasi – Ƙwararren masanin nukiliya kuma tsohon shugaban Hukumar Makaman nukiliyar Iran
- Mohammad Mahdi Tehranchi – Ƙwararren masanin nukiliya, wanda kuma ke da hannu a shirin makaman nukiliyar ƙasar.
- Mohammad Bagheri – Shugaban ma’aikatan sojin Iran
Rahotannin kafofin yaɗa labaran Iran sun ce harin Isra’ila ya kuma jikkata Ali Shamkhani, babban mai bai wa shugaban addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei shawara. In ji BBC.