Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito gwamnatin Isra’ila, na kira ga ‘yan ƙasarta da ke zaune a ƙasashen Masar da Jordan su yi bakin ƙoƙarinsu domin barin ƙasashen biyu.
Wata sanarwar da AFP ya samu daga majalisar tsaron Isra’ila, ta ce “muna gargaɗi ga mai ƙarfi ga masu yin tafiye-tafiye zuwa Masar (ciki har da Sinai) da kuma Jordan. Muna kira ga mutane kada su je waɗanan ƙasashe, kuma waɗanda ke cikin ƙasashen a halin yanzu, su yi ƙoƙarin fita daga cikinsu”.
A farkon wannan makon ma, Isra’ila ta yi wa ‘yan ƙasarta da ke zaune a Turkiyya makamancin wannan gargaɗi.


