Isra’ila ta zargi Canada da taimaka wa Hamas bayan sanar da shirinta na amincewa da ƙasar Falasdinu – kasa ta uku da ta sanar da matakin a cikin yan kwanakin nan.
Firaministan Canada, Mark Carney, ya ce yana fatan samar da ƙasashe biyu domin tabbatar da samar da zaman lafiya.
Ya ce matakin zai faru ne a watan Satumba idan har hukumomin Falasɗinawa suka gudanar da sauye-sauyen dimokradiyya.
Matakin na Canada bayan na Faransa da Birtaniya ya ci gaba da mayar da Amurka saniyar ware a goyon bayan da take ci gaba da bai wa Isra’ila a yakin Gaza.
Shugaba Trump ya yi gargaɗin cewa shawarar da Canada ta yanke zai zamar mata wahala wajen ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da Amurka.