Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta musanta dangantaka da mutumin da ya caka wa Salman Rushdie wuka.
Mai magana da yawun ma’aikatar, Nasser Kanaani, ya ce marubucin da kuma magoya bayansa ke da alhakin harin saboda batanci ga addinin Musulunci.
Har yanzu Mr Rushdie na cikin halin rai kwa-kwai-mutu-kwa-kwai bayan caka masa wukar da aka yi a lokacin da yake kan dandamali don gudanar da jawabi a wani taron marubuta a birnin New York na Amurka a ranar Jumma’a.
Ko da yake a yanzu yana iya numfashi.
Martanin Iran din ya zo ne bayan sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi tir da hukumomin Iran saboda ingiza bore kan marubucin.
A ranar Lahadi gwamnan New York, Kathy Hochul, ta ce mutumin da ke dauke da wuka ba zai rufe bakin mai dauke da alkalami ba.
Mutumin da ake zargi dai bai amsa tuhumar da ake masa ta yunkurin kisa ba. In ji majiyar BBC.


