Hukumar zaɓe mai zaman kanta na Najeriya INEC ta ce an ƙara adadin rumfunan zaɓen da za a yi amfani da su a lokacin zaɓen gwamnan Jihar Osun.
A wani saƙo da INEC ɗin ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce an ƙara adadin rumfunan zaɓen zuwa 3,763 a maimakon 3,010 da ake da su a baya.
A ranar 16 ga watan Yulin nan ne dai ake sa ran gudanar da zaɓen gwamnan jihar.
Cikin waɗanda za su fafata akwai Yusuff Lasun na Labour Party da Akin Ogunbiyi na Accord Party da Gboyega Oyetola na APC Ademola Adeleke na PDP da Omigbodun Akinrinola na SDP.