Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ki amincewa da zaben fidda gwanin da ya samar da Sanata Godswill Akpabio, a matsayin dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a gundumar Akwa Ibom ta arewa maso yamma.
Akpabio, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, a daren ranar Talatar da ta gabata, a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar, ya janye takararsa na tsayawa takarar shugaban kasa na amincewa da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
A ranar 27 ga Mayu, 2022, Ekpoudom ya lashe zaben fidda gwani na Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma domin samun tikitin APC.
Sai dai shugaban jam’iyyar na jihar, Stephen Ntuekpo, yayin da yake bayyana rashin tsaro a zaben fidda gwani na ranar 27 ga watan Mayu a gundumar, ya yi ikirarin cewa hedkwatar jam’iyyar APC ta kasa ta umurce shi da ya gudanar da wani sabon zaben fidda gwani a ranar 8 ga watan Yunin 2022.
Zaben fidda gwanin da aka yi ya haifar da Sanata Akpabio a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani. Ya samu kuri’u 478 daga cikin wakilai 512 da aka amince da su.
Sai dai kwamishinan zabe na jihar Akwa Ibom Mike Igini ya ce hukumar za ta amince da wanda ya lashe zaben fidda gwani da INEC ta sanyawa ido. A cewra The Will.
Igini, wanda ya zanta da Aminiya a ranar Lahadi a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, ya musanta ikirarin cewa hukumar ta sa ido a kan zaben fidda gwani na ‘yan majalisar dattawa na APC, inda Akpabio ya yi nasara.