Gwamna Umar Abdullahi Ganduje na jihar Kano, ya taya zababben gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP murna, amma ya gargade shi da cewa zai gudanar da ‘yar gajeruwar gwamnati, don haka za su haɗu a kotu.
Ganduje, wanda ke gabatar da addu’o’i ga shugaban kasa mai jiran gado, Bola Ahmad Tinubu a bikin cikarsa shekaru 71 a gidan gwamnati, ranar Asabar, ya ce, yana taya Yusuf murnar samun ‘yar gajeriyar nasara a zaben da ya gabata.
Karanta Wannan: A dakata da baiwa gwamnatin Kano bashi – Abba
Ya ce, tun daga lokacin ne suka umarci lauyoyinsu da su shirya matakan shari’a a kan sakamakon zaben da ya tabka kura-kurai da magudi.
Sallar ta samu halartar shuwagabannin musulunci na bangarori daban-daban tare da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da sauran su. In ji Daily Post.