Jam’iyyar Conservative mai mulki a Birtaniya ta fara hutun ƙarshen mako cikin zazzafar siyasa a yunƙurin da take yi na zaɓen sabon Firaiminista bayan murabus ɗin Liz Truss.
Waɗanda ke zawarcin kujerar na da zuwa Litinin su samu goyon bayan ƴan majalisa.
Ana buƙatar wanda zai nemi tsayawa takarara firaiminista ya sami aƙalla yan majalisa 100 na goyon bayansa.
Tuni dai Rishi Sunak ya ce ya kusan kai wannan adadi.
Sai dai hankalin jama’a ya karkata kan tsohon firaiminsta Boris Johnson wanda zai koma Landan daga yankin Caribbean inda ya tafi hutu.
Rahotanni sun ce Mista Johnson ɗin ya ƙenƙyasa wa wani makusancinsa cewa a shirye yake ya fito takara.


