fidelitybank

Idan ba ka sanya makarin hanci da baki ba za ka biya Riyal 1000 – Saudi

Date:

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya ta yi gargaɗin cewa, za a ci tarar waɗanda su ke saɓawa dokokin da a ka saka na yaƙi da annobar korona.

Jaridar Saudi Gazette ta rawaito cewa, ma’aikatar ta ce ƙin saka takunkumi ko ƙyalle, domin rufe baki da hanci babban laifi ne wanda zai iya jazawa mutum ya biya tarar riyal 1000.

Ma’aikatar ta bayyana cewa, za a ci gaba da ruɓanya kuɗin idan mutum ya ci gaba da saɓawa dokar, har kuɗin su kai riyal dubu 100.

Tun daga Alhamis ɗin da ta gabata ne dai kasar Saudiyya ta kara saka dokokin kiyaye yaɗuwar korona, kamar saka takunkumi da bayar da tazara a daidai lokacin da a ke cikin fargabar yaɗuwar sabon nau’in korona na Omicron.

 

 

sani ahmad

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Dino Melaye ya gudu daga PDP ya faɗa ADC

Tsohon ɗan jamalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Yamma,...

Isra’ila na zargin Canada da goyon bayan Hamas – Netanyahu

Isra'ila ta zargi Canada da taimaka wa Hamas bayan...

Rashin tallafin agaji ka iya dawo da Boko Haram a Najeriya – MDD

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta...

Yin gini a kan hanyoyin ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa da Najeriya NEMA ta...

Amnesty ta yi Allah wadai da tsare Sultan kan bidiyon lafiyar Tinubu

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi...

Dalilin da ya sa na gana da Tinubu – Kofa

Ɗan majalisar tarayyar mai wakilitar Kiru da Bebeji daga...

Ba za mu jingine yajin aiki ba har sai an biya mana buƙatun mu – Ma’aikatan Jinya

Shugaban ƙungiyar ma'aikatan jinya ta Najeriya, Morakinyo-Olajide Rilwan ya...

Za a fara yi wa Dalibai gwajin kwaya kafin su shiga jami’a – NDLEA

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta fara yi wa...

Za mu kammala titin jirgi na Kaduna zuwa Kano a 2026 – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya, ta ce za a kammala aikin titin...

Adadin kudaden da Liverpool ta kashe wajen daukar ‘yan wasa

Liverpool ta kashe fam miliyan 265 wajen ɗauko ƴanƙwallon...

Sunderland ta ɗauko ƴanƙwallo bakwai a kakar bana

Granit Xhaka ya zaman ɗan ƙwallo na bakwai da...

James Trafford ya sake komawa Man City daga Burnley

Mai tsaron ragar tawagar Ingila, mai shekara 21, James...
X whatsapp