fidelitybank

Idan ba a dauki mataki a kan kisan Hanifa ba zamu shige gaba – Human Right

Date:

Kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta ce matuƙar ba a ɗauki matakin da ya dace akan Abdulmalik Muhammad Tanko da ake zargi da kashe Hanifa Abubakar, za su shige gaba domin yin abinda ya dace.
Jami’in hulɗa da jama’a na kungiyar, Muhammad A-A King, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar mai ɗauke dasa hannunsa aka rabawa manema labarai a rana Asabar.
Ya ce “Munsan dukkanin irin abubuwan da suke faruwa a ƙasar nan na ƙarancin ɗaukar mataki akan al’amarin makamancin na Hanifa da ya faru, domin haka muke kira da kakkausar murya da a ɗauki matakin da ya dace akan kisan Hanifa Abubakar ko kuma mu wuce gaba har muga an ɗauki matakin da ya dace,” in ji A-A King.
Hakazalika Shugaban Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam, Ambasada Karibu Yahya Lawan Kabara, ya ce, matuƙar jami’an tsaro da ma’aikan shari’a harma da ɓangaren gwamnatin Kano ba su ɗauki matakin da ya dace ba, babu shakka za su ɗauki matakin doka a duk ɓangaren da aka samu sakaci.

bbc news nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp