fidelitybank

Hukumomin tsaro ku gaggauta magance matsalar tsaro a Najeriya – Majalisa

Date:

Majalisar Dattiai ta bai wa manyan hafsoshin tsaron kasar nan wa’adin wata hudu su kawo karshen matsalolin tsaron da ke addabar sassan kasar.

Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ta yi wata doguwar ganawa da shugabannin a jiya, duk da cewa majalisar tana hutu.

A baya-bayan nan dai lamarin tsaro ya sukurkuce, al’amarin da ya kai ga wasu ‘yan majalisar yunkurin tsige Shugaba Muhammadu Buhari muddin bai sauya salo ba.

Majalisar dokoki, ta bayyana tsor da damuwarta game da ƙaruwar rashin tsaro a ƙasar, musamman harin da ƴan ta’adda suka kai kwanan nan a Abuja.

Shugaban majaliar dattijai, Ahmad Lawan, ya kira shugabannin tsaro taron gaggawa a jiya, inda ya ce lamari ne mai ban tsoro.

A taron, sanatoci sun bai wa shugabannin tsaro shawarwari a kan yadda za a kare Birnin Tarayya da ƙasar gaba daya.

Mafi yawan kwamitocin majalisar dokokin su ma sun gana da shugabannin tsaro akan matsalolin tsaron a Juma’ar da ta wuce don sanin me ake ciki a ƙasar.

Majalisar wakilai ta ce, ƴan ta’adda suna barazanar kai hari Abuja, inda fadar shugaban ƙasa take, inda suka ce dole hukumomin tsaro su yi maganin masu tayar da ƙayar bayan.

A cikin makonnin da suka wuce, birnin tarayya ya fuskanci barazana daga wurin ƴan ta’adda akan kai hari kan wasu dakarun sojji da gidan yarin Kuje.

A ranar Alhamis ɗin da ta wuce ma, ƴan ta’adda sun kai wa sojojin da ke shingen bincike na Dutsen Zuma mai nisan kilomita kadan daga cikin birnin Abuja.

the sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp