fidelitybank

Hukumar tattara haraji ta Kano ta rabawa ma’aikata 200 takardar tuhuma

Date:

Hukumar tattara haraji ta jihar Kano, (KIRS) ta rabawa ma’aikatanta takardar tuhuma sama da mutane 200.

Shugaban hukumar, Abdurrazak Datti Salihi ne ya bayar da wannan takardar  tuhumar tun a ranar jumaa da ta gabata, ya yin rangadi da ya yi a ofishin hukumar da misalin karfe 5:20 na yammacin Juma ar.

Takardar da shugaban ya bayar ga ma’aikatan, ta kunshi bayani kamar haka. An lura cewa ba ka kan kujera a lokacin da shugaban hukumar ya kawo maka ziyara a ofishin ka a ranar Juma’a, 17 ga Disamba, 2021

Bisa la’akari da abubuwan da ke sama, ya kamata ku bayyana dalilin da ya sa baka nan, domin za a dau matakin ladabtarwa a kanka.

Wasu daga cikin ma’aikatan sun bayyana cewar ranar Litinin da Juma a shugaban ya yi rangadi bayan karfe 5 na yamma lokacin wasu sun tashi wasu kuma suna wajen aiki a waje domin duba da cewar aikin na su yawanci ba na zama bane su na yawace-yawace wajen tattara kudaden haraji, Iokacin da ya zo ba mitune shi ne ya dauki sunayen wadanda su ke nan daga bisani wadanda bai same su ba a ka bisu da takardar tuhuma (Query) su sama da dari 200.

naija legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp