fidelitybank

Hukumar samar da aiki ta kasa ta horas da matasa 50 a Kano

Date:

Hukumar samar da aikin yi ta kasa (NDE) ta fara aiwatar da wani horo na kwanaki biyar ga matasa da mata 50 da ba su da aikin yi a Kano a kan aikin noma.

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar ranar Litinin a Kano, Kodinetan NDE na jihar, Malam Idris Sani Yakasai, ya ce, makasudin gudanar da horon shi ne samar da ayyukan yi ga matasa.

Ya kara da cewa hakan zai taimaka “Domin inganta hanyoyin noma da ke da alaka da ayyukan noman gargajiya da kuma kara samar da abinci a jihar da kuma tarayya.”

Ko’odinetan ya ce, horon ya kuma yi da nufin rage ci rani zuwa wasu garuruwan da matasa ke yi.

Ya kara da cewa, NDE na da niyyar ba su wasu rancen kudade domin sayen injuna, wanda zai ba su damar shiga cikin karkara.

Yakasai ya ce,”Wadanda aka horas din kuma za a dauki su a matsayin masu sana’o’in dogaro da kai, domin za su iya karban wasu kudade ga manoman don ayyukan”. In ji Yakasai.

Saifullahi Sulaiman, daya daga cikin mahalarta taron, ya godewa gwamnatin tarayya bisa irin wannan horon, sannan ya yi alkawarin aiwatar da abin da suka koya a karshen kwas din.

Sai dai ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara yawan wadanda za su halarci horon na gaba, ya kuma bukaci gwamnatin jihar ta yi hakan, domin kara samar da ayyukan yi.

Shi ma Abdul-Rasheed Mohammed, wani mahalarci, ya yaba da wannan karimcin, ya na mai cewa, “Horon ya dace da ni don dogaro da kai da kuma samar da aikin yi.”

legit.ng.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp