fidelitybank

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Date:

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a shekarar 2024, ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776, tare da warware rikicin aure 621. Haka kuma hukumar ta tara kuma ta raba kuɗaɗen tallafi da bashin da aka gaza biya da ya kai Naira miliyan 212,334,839.

Kwamandan rundunar, Sheikh Amin Ibrahim Daurawa, ya ce tun bayan zuwan Gwamna Abba Kabir Yusuf a ranar 29 ga Mayu, 2023, an inganta harkokin Hisbah domin ciyar da ayyukanta gaba.

Ayyukan da hukumar ta gudanar sun haɗa da:

Auren Gata ga ma’aurata 3,800.
Horon ƙwarewa ga jami’an Hisbah 1,000.
Rabon kayan tallafi ga marayu, gwauraye da gajiyayyu.
Taimakawa wajen aikin Hajji daga Kano zuwa Saudiyya.
A halin yanzu, rundunar tana da fiye da jami’ai 4,000 da ke aiki a kananan hukumomi 44 na jihar, tare da sassan ayyuka da dama ciki har da bangaren mata karkashin jagorancin Dr. Khadija Sagir Suleiman.

Gwamnatin Kano ta bayyana shirin kafa makarantar horar da jami’an rundunar, ƙara albashi da tsarin ritaya ga jami’an Hisbah, sabbin kayan aiki da kuma gina sabuwar hedikwatar hukumar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa Hisbah don tabbatar da adalci, zaman lafiya da ɗorewar ɗabi’u masu kyau a Kano.

www nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp