fidelitybank

Harin Sokoto: Gwamnati na bukatar goyon bayan ‘yan Najeriya – Buhari

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikinsa a kan harin da aka kai wa wasu matafiya da ba su ji ba, ba su gani ba a jihar Sokoto.

Sanarwar da fadar shugaban ta fitar a ranar Laraba na cewa, Muhammadu Buhari ya damu matuka da yadda waɗannan ƴan kasa da ba su ji ba, ba su gani ba suka gamu da ajalinsu a kan hanyarsu ta neman halal.

Akalla mutum 21 ƴan bindiga suka ƙona a wata motar fasinja lokacin da su ka yi musu kwanton-bauna a ranar Talata. A cewar BBC.

Sai dai wasu ‘yan uwan fasinjojin sun ce mutanen da ‘yan bindigar suka kona sun kai mutum 42.

Rahotannin sun ce fasinjojin sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar, domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Najeriya, saboda ta’azzarar hare-haren ‘yan bindiga a inda suke.

Buhari ya jajantawa iyalan waɗanda aka kashe tare da cewa jami’an tsaro za su ci gaba da koƙari na kawo ƙarshen waɗannan miyagun mutane.

Ya ce wannan mummunan al’amari da gwamnatinsa ke fuskanta na buƙatar goyon bayan dukkanin ƴan Najeriya.

nigeria legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

A na neman kusan Mutane 400 da suka ɓace a ambaliyar Neja

A na ci gaba da ayyukan ceto bayan ambaliyar...

Mun bayar da hutu ranar Litinin bisa jimamin mutuwar ƴan Wasa – Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar...

Tun farko na shaida wa Tinubu ba zan zaɓe shi ba – Amaechi

Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce...

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka ƴan Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aƙalla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...
X whatsapp