fidelitybank

Gwamnatin Kano ta na asarar Naira miliyan 378 a kan zaizayar kasa – Dr Gawuna

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa jihar na asarar Naira miliyan 378 a duk shekara, sakamakon zaizayar kasa karkashin aikin noman Watari.

Mataimakin gwamnan jihar, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya shaidawa manema labarai jiya a Kano, yayin wani taron manema labarai.

Ya shaida cewa: “Akwai aikin noman ruwa na Watari da aka kammala mai fadin hekta 962 daga cikin kashi 40 cikin 100 ko kuma 384 ba a yi amfani da su a baya ba, saboda lalacewar madatsar ruwa da kayayyakin more rayuwa a can. Amma saboda wannan aikin, APPEALS, ana amfani da shi sosai.

“Akwai kuma gyaran da aka yi na hekta 150 da aka yi a baya, sakamakon zaizayar kasa. An kiyasta asarar hekta 150 a duk shekara ya kai Naira miliyan 378. Sakamakon fadadawar Watari a yanzu haka ta kai hekta 1,000, kuma manoma kusan 4,000 ne za su amfana kai tsaye. Tare da fadada, mun kara amfani da filin noman Watari. Duk da cewa an yi amfani da shi, za mu kaddamar da aikin nan ba da dadewa ba, saboda aiki ne mai matukar muhimmanci,” in ji Gawuna.

Dangane da korafin da manoman jihar suka yi kan rufe madatsar ruwan Tiga da suka ce, ya yi barazana ga ayyukan noman ban ruwa, mataimakin gwamnan ya ce, ana sa ran kammala aikin dam a tsakiyar wannan shekara.

Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ke rike da mukamin kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar, ya ce, an rufe dam din ne domin a samu damar yin gyare-gyare a madatsar, domin samun cikakken amfani da bunkasa ayyukan noman ban ruwa a yankunan.

vgn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp