fidelitybank

Gwamnatin Kano ta kulla yarjejeniya da kasar Saudiyya na horar da malamai 5,000

Date:

Gwamnatin jihar Kano karkashin Dr. Abdullahi Ganduje ta amince da wata yarjejeniya tsakanin Kano da Madina Academy da ke kasar Saudiyya, domin horar da malamai 5,000 a Madina.

Gwamnatin jihar za ta dauki nauyin bayar da tikitin dawowar jirgi, biza, alawus na horo ga rukunin farko na malamai 50 da za su halarci babban horo a Madina kafin watan Ramadan.

Gwamnatin ta kuma amince da fitar da Naira miliyan 94.9 domin saukaka matsugunin shagunan haya da gareji a kasar Saudiyya na shekarar 2020 da 2021.

A halin da a ke ciki, gwamnatin Ganduje ta kuma amince da Naira miliyan 500 a matsayin asusun tallafi na shekara shida na bankin duniya, mai suna ‘Agro Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL)’.

Kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba ne ya sanar da hakan a yayin ganawa da manema labarai kan sakamakon taron majalisar zartarwar jihar na jihar.

Ya yi bayanin cewa aikin na da nufin kara daukar sabbin hanyoyin magance yanayi da inganta rayuwa tare da magance kwaranyowar hamada a Arewacin Najeriya.

Aikin zai karfafa nasarorin da a ka samu a karkashin shirin kula da zaizayar kasa da ruwan sha ta Najeriya (NEWMAP) a Kano.

Kwamishinan ya ci gaba da bayyana cewa majalisar ta amince da kwangilar kammala aikin gyaran hanya mai tsawon kilomita biyar a karamar hukumar Tofa.

Wani amincewa kuma shine domin sakin kudade don horar da ma’aikatan kiwon lafiya da kuma mayar da tallafin asusun ilimi mai kunshe da stamfi.

Ya kara da cewa majalisar ta amince da sabunta sadarwar intanet da kuma kula da kayan aikin fasahar ICT mai kunshe da bayanan hukumar lura da asibitoci (HMIS) wanda za kuma a sanya manhajar software a asibitin koyarwa na Abdullahi Wase.

Sauran sun kasance masu ba da shawara ne domin kula da shirin samar da hanyoyin sadarwa na Fiber Optics na jihar Kano da kuma siyan motocin kashe gobara.

the nation newspaper 
today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp