fidelitybank

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da ‘yan kasuwar Kano da ba a tantance adadin su ba

Date:

Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ‘yan kasuwar Kano wadanda ba a tantance adadinsu ba, a kusa da dajin Ungwan Yako da ke karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna a ranar Laraba.

Wata majiya ta bayyana cewa, ‘yan bindigar sun tare babbar hanyar ne a daidai lokacin da ‘yan kasuwar ke tafiya Kano daga Brinin Gwari inda a ke zargin su da kai wadanda harin ya rutsa da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Hanyar Birin zuwa Gwari, a tsawon shekaru, ta zama tarkon mutuwa ga masu ababen hawa da matafiya, sakamakon munanan ayyukan ‘yan bindiga da su ka addabi hanyar, wadda ta kasance hanyar shiga yankin Kudu maso Yammacin kasar nan zuwa jihar Kaduna.

PUNCH ta rawaito cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin tare da yin awon gaba da ‘yan kasuwa sama da 70 daga Kano a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna a ranar 22 ga Disamba, 2021.

Sai dai rundunar ‘yan sanda a Kaduna cikin kasa da sa’o’i 24, ta tattara tare da kubutar da 48 daga cikin wadanda lamarin ya shafa, yayin da wata mace da a ka kashe ba a san inda ta ke ba har zuwa yau.

Har yanzu dai ba a tabbatar da faruwar lamarin ba, ko dai daga gwamnatin jihar ko kuma rundunar ‘yan sandan jihar.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammad Jalige, bai amsa kiransa ba ko kuma amsa sakon wayarsa.

Majiyar ta ce wadanda harin ya rutsa da su sun yi tattaki ne daga Birnin Gwari inda suka je Kano kafin masu garkuwar su tafi da su.

A cewarsa, wasu matafiya sun ga motocin da babu kowa a gefen hanya, inda ya kara da cewa maharan na shiga cikin dajin Yako mai firgita.

taraba state today news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...

Ba mu kai wa Isra’ila hari ba – Iran

Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ƙasar...

Duk da faduwar farashin mai NNPCL ya kara farashi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin...

Duk wasu ƙawayen Amurka za su ɗanɗanar kuɗarsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...

Iran ta mayar da martani kan sojojin Amurka dake Qatar

Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ƙasar ta...

Faransa ba ta goyon bayan Amurka na kifer da gwamnatin Iran – Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce, ƙasarsu ba ta...

Kotu a Kano ta ɗaure masu satar Yara

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller...

Ba wata hujja da Amurka za ta kai wa Iran hari – Rasha

An gudanar da tattaunawa tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin...

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...
X whatsapp