Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan inda aka kai wajen hukunta wadanda aka kama bisa zargin samar da kudi ga mayakan Boko Haram.
A watan Fabrairun bana ne ta ce ta gano wasu mutane da kamfanoni kimanin dari daya dake samar da kudade ga kungiyar ISWAP tare da kama 45 daga cikinsu.
Daga bisani wasu bayanai daga hukumomin tsaron kasar suka tabbatar da gudanar kamen ‘yan canji kusan 400 a wasu jihohi kimanin 8 bisa irin wannan tuhumar.
Sai dai a yayin da ‘yan Najeriya ke saka ayar tambaya kan yadda aka ji shiru na tsawon watanni kan wannan maganar.
Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya shaidawa BBC cewa, tuni aka yi nisa ga bincike kuma har an saki wasunsu da aka gano ba su da hannu a lamarin:


