Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar wa da manoman cewa, za a kammala aikin madatsar ruwa ta Tiga nan da watan Yuni na wannan shekara.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Talata.
Gawuna wanda ya yi tsokaci kan koke-koke da manoman rani a jihar Kano ke yi, kan rufe madatsar ruwan Tiga, ya bayyana cewa”An rufe madatsar ruwan ne, domin baiwa hukumomin da ke sa ido damar gudanar da gyare-gyare a tashoshin”.
Ya ce, “Dole ne mu rufe madatsar ruwa ta Tiga, domin a samu damar yin gyare-gyare. Ko da ya ke ba gwamnatin jihar Kano ce, ta yi aikin rufe bakin ba, sai dai hukumar raya kogin Hadeja Jamare”.
“Tun tsawon wadannan shekaru, muna jinkiri wajen aiwatar da kwangilar gyarawa da kuma tsawaita aikin noman ruwa da wani kamfani mai suna “Transforming Irrigation Management in Nigeria, TRIMMING” ke yi. Dole ne mu kyale su su rufe dam”.
Mataimakin Gwamnan wanda kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar ya bayyana cewa, gyaran hanyoyin da aka gyara za su bunkasa ayyukan noman ban ruwa a yankunan.